Dan takarar gwamna a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Kaduna, Mai Girma Rt. Hon. Shehu Bawa ABG, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan dattijon kasa, Alhaji Rabiu Bako, wanda ya rasu kwanan nan a Kaduna.
Ziyarar ta gudana ne a gidan marigayin da ke Kaduna, inda ’yan uwa, abokan siyasa da sauran masu alhini suka tarbi Hon. Shehu ABG domin jimamin rasuwar fitaccen jagoran al’umma.
Da yake jawabi yayin ziyarar, ABG ya bayyana matukar alhininsa kan rasuwar dattijon, inda ya bayyana marigayi Rabiu Bako a matsayin gogaggen dan siyasa kuma jagora mai kishin hadin kan al’umma, wanda gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban da hadin kan Jihar Kaduna ba za ta taba mantuwa ba.
Ya ce marigayin ya yi fice wajen hikima, tawali’u da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, yana mai cewa shawarwarinsa da kulawarsa ta uba sun taka muhimmiyar rawa wajen tsara tafiyar siyasa da kyautata alakar al’umma a fadin jihar.
Dan takarar gwamnan ya kara da cewa rayuwar Rabiu Bako ta kasance cike da hidima ga jama’a da bunkasa rayuwar al’umma, yana mai jaddada cewa abin koyi da ya bari zai ci gaba da zaburar da matasa da shugabanni masu tasowa a nan gaba, a Kaduna da ma kasa baki daya.
ABG ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa tare da ba shi Aljannatul Firdaus, ya kuma roki ’yan uwa da su dauki hakuri tare da yin juriya, su samu kwarin gwiwa daga kyakkyawar rayuwar da marigayin ya yi da kuma irin soyayyar da ya samu daga jama’a.
Har ila yau, ya ba iyalan tabbacin cewa zai ci gaba da tsayawa tare da su a wannan lokaci na jimami, yana mai jaddada muhimmancin hadin kai da tausayi a irin wannan hali na alhini.
A nasa jawabin, Hon. Sani Rabiu Bako, wanda ya yi magana a madadin iyalan, ya gode wa ABG bisa ziyarar da ya kai da kuma nuna goyon baya a wannan lokaci mai wuya, yana mai cewa hakan alama ce ta shugabanci na gari da kuma tausayi na hakika.
Masu sa ido kan harkokin siyasa sun bayyana cewa ziyarar ta’aziyyar na kara nuna kudurin Hon. Shehu ABG na tsayawa tare da al’ummar Jihar Kaduna a lokutan farin ciki da kuma bakin ciki, tare da karfafa sakonsa na hadin kai, tausayi da shugabanci mai rungumar kowa.