Hon. Mahmood Mamman Lagos ya bayyana aniyarsa a hukumance ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna domin wakiltar mazabar Doka/Gabasawa a zaben shekarar 2027 karkashin inuwar Jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai sakatariyar jam’iyyar APC ta Karamar Hukumar Kaduna North, inda ya gana da shugabannin jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki domin sanar da su kudurinsa na tsayawa takara.
A yayin ziyarar, shugaban jam’iyyar APC na Kaduna North, Suleiman Wada Usman, tare da sauran ‘yan kwamitin zartarwa na jam’iyyar sun tarbe shi hannu bibbiyu tare da nuna farin cikinsu da wannan buri nasa.
Da yake jawabi a wurin, Hon. Lagos ya ce babban dalilin zuwansa ofishin jam’iyyar shi ne domin taya sabbin shugabannin jam’iyyar murnar samun nasarar da suka samu, tare da sake jaddada kudurinsa na karfafa jam’iyyar APC a matakin kasa.
Ya bayyana cewa shawarar da ya dauka ta neman kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta samo asali ne daga burinsa na samar da wakilci nagari da kuma yin aiki tukuru domin ci gaban al’ummar Doka/Gabasawa.
A cewarsa, yana da kwarewa, gogewa da kuma kusanci da al’umma wanda zai ba shi damar kare muradun jama’a tare da bayar da gudunmawa mai ma’ana wajen bunkasa ayyukan majalisa a jihar.
Hon. Lagos ya kuma sake jaddada cikakken goyon bayansa ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, inda ya bayyana Ajandar Ci Gaba Mai Dorewa ta gwamnan a matsayin wata manufa mai anfani wadda za ta kawo sauyi mai kyau a jihar.
“Ina bayar da cikakken goyon baya dari bisa dari ga Ajandar Ci Gaba Mai Dorewa ta Gwamna Uba Sani, kuma zan ci gaba da aiki tare da shugabannin jam’iyya da dattawan APC domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a fadin Jihar Kaduna,” in ji shi.
Dan takarar ya kuma tabbatar wa shugabannin jam’iyyar cewa zai ci gaba da bin ka’idojin hadin kai, biyayya da ladabi a cikin jam’iyyar, yana mai cewa burinsa na siyasa yana da nufin karfafa APC da kuma kare muradun dukkan mambobinta.
Hon. Mahmood Mamman Lagos ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati, abokan siyasa da magoya bayan jam’iyya a wannan ziyara, inda suka bayyana amincewarsu da kwarewarsa tare da yin alkawarin mara masa baya a zaben shekarar 2027.