Rushewar Masallacin Jumma’ar Zaria: Sardaunan Badarawa Ya Mika Ta’aziyya ga Gwamna Uba Sani, Sarkin Zazzau da Iyalan Mamata

Honorabul Usman Ibrahim wanda aka fi sani da Sardaunan Badarawa ya bayyana kaduwa tare da alhinin abun da ya faru a babbar masallacin Jumma’a ta garin Zaria inda masallata da dama Suka rasa rayukansu yayin da ginin wurin ibada ya ruguzo musu a ka.

A wata sanarwa da Sardaunan Badarawa ya sanya ma hannu dan siyasar ya ce hatsarin masallacin Zaria abu ne da ya tada hankalin shi matuka, amma ya nuna cewa masallatan sun yi shahada ne wanda ya ce burin kowane Musulmi ne.

Bayan addu’a ga wadanda suka rasu cikin hatsarin Sardaunan Badarawa wanda kuma shi ne Santurakin Hausa ya yi tsokaci da cewa Najeriya ta yi babban rashi sabida ko ba komai an rasa wadanda suke yi ma Kasa adduoi ta fita daga kuncin rayuwar da talaka yake fama da shi.

“Ina mika ta’aziya ta ga Gwamna Uba Sani da Sarkin Zazzau Ambasada Nuhu Bamali da daukacin mutanen da suka rasa yan uwansu a masallacin garin Zaria.

“Ina fatan Allah Ya karbi shahadar su ya kuma baiwa wadanda suka bari hakuri da juriyar rashin yan uwansu da iyayensu.

“Muna rokon Allah Ya kiyaye afkuwar irin wannan ibtilain daga cikin alummanmu, ” Ya roki Allah.